An ranstar da Al-Sisi sabon shugaban Masar

Image caption Al-sisi dai zai gaji wata kasa da kawunan 'ya'yanta suka rarraba kuma ta galabaita.

An rantsar da Abdulfatah Al-sisi a matsayin sabon shugaban Masar a babban birnin kasar Alkahira, cikin tsauraran matakan tsaro.

Tsohon babban hafsan sojin ya samu kashi 97% na kuri'un da aka jefa a zaben da fiye da kashi 50% na masu jefa kuri'a ba su fito ba.

Wata wakiliyar BBC a babban birnin kasar Alkahira ta ce masu goyon bayan Al-sisi na fatan zai ba marada kunya ta fannin samar da tsaro da kawo cigaban tattalin arziki; yayinda masu adawa da shi ke fargabar cewa zabensa zai sake mayar da kasar karkashin mulki mulaka'u.

Masu sharhi na ganin cewa idan ya kasa fitar da kasar daga cikin halin ta shiga, shi ma zai iya fuskantar bore kamar wadanda ya gada.

Karin bayani