Za'a ci gaba da bincikar FIFA

Qatar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugabannin FIFA sun musanta karbar na goro a hannun Bin Hammam

Kamfanin laturoni na Sony wanda ke kan gaba wajen daukar nauyin gasar wasan kwallon kafa ta duniya, ya yi kira da a gudanar da bincike game da zargin da ake yi na bada na goro domin kasar Qatar ta samu karbar bakuncin wasan da za a yi a shekarar 2022.

A makon da ya gabata ne Jaridar Sunday Times ta Burtaniya ta wallafa labarin da ke cewa tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta FIFA a Qatar Muhammad Bin Hammam ya ba wa shugabannin da ke shirya gasar miliyoyin daloli domin su marawa kasar sa baya dan samun bakuncin wasan, sai dai kwamitin FIFA ya musanta wannan batu.

A yau kuma jaridar ta yi zargin cewa Bin Hamma ya yi amfani da karfinsa na fada aji wajen samarwa Qatar goyon baya, da kuma shirya wata ganawa tsakanin shugabannin FIFA da 'yan gidan sarautar Qatar duk kan batun.