Wa zai gaji Ado Bayero?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masautar Kano dai daya ce daga cikin masarautun da suka fi saura girma a arewacin Najeriya.

Bayan binne gawar marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, a yanzu hankalin 'yan gidan sarautar Kano ya karkata ne ga wanda zai gaje shi a matsayin sarki.

Akan dai zabo Sarkin Kano ne daga zuriyar gidan Malam Ibrahim Dabo, abin da ke nufi cewa mutane masu yawa na da damar neman gadon kujerar.

Mutane hudu ne dai da ke rike da wasu manyan sarautu a masarautar ke zabar Sarki a Kano, da suka hada da Madakin kano, da Sarkin Bai, da sarkin Dawaki mai tuta, da kuma Makama; sai dai ko da sun yi zaben sai gwamnati ta amince da wanda suka zaba tukuna kafin ya zama sarkin.

Kowane lokaci daga yanzu dai masu zaben sarkin za su iya sanar da wanda suka zaban a zaman sabon sarkin Kanon.

Karin bayani