An yanke ma wasu hukuncin kisa a Masar

Wasu mutane a harabar kotu a Masar
Image caption Wasu mutane a harabar kotu a Masar

Kotu a Masar ta yanke hukuncin kisa a kan shugabanni goma na kungiyar 'Yan'uwa Musulmi da aka haramta a kasar, bisa iza wutar tashin hankali, inda mutane biyu suka rasu a watan Yuli.

Muhammad Al Beltagy, kusa a Kungiyar 'Yan'uwa Musulmi, da ke cikin kejin tuhumammun, ya yi ta daga murya yana Allah wadai da masu shari'ar kasar.

Ya zarge su da bautar da jama'a, da mayar da su karkashin sojoji.

Mutane talatin da takwas ne dai aka gurfanar, sauran, da suka hada da jagoran kungiyar Muhammad Badie, za a yanke masu hukunci nan gaba.

Kodayake dama an yanke masa hukuncin kisa.