An rantsar da sabon shugaban Ukraine

Sabon shugaban kasar Ukraine Petro peroshonko Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mr Peroshonko ya lashe zaben da aka gudanar a watan da ya gabata a kasar Ukraine

An rantsar da hamshakin attajirin nan mai kamfanonin kayan kwalam da makulashe Petro Poroshenko a matsayin sabon shugaban kasar Ukraine a yayin wani biki a zauren majaliasar dokokin kasar da ke birnin Kiev.

Shi dai Mr. Poroshenko ya yi nasarar lashe zaben da aka gudanar a kasar a watan da ya gabata, kuma yana son kara karfafa danganta ka tsakanin Ukraine da kungiyar tarayyar turai.

Ya kuma yi alkawarin kawo karshen rikicin da ake tsakanin dakarun sojin Ukraine da 'yan tawaye 'yan aware magoya bayan Rasha a gabashin Ukraine sai dai bai bayyana yadda zai magance matsalar ba.

A jiya juma'a ne Mr Poroshenko ya gana da shugaban Rasha Vladimir Putin a wani bangare na fara sasantawa tsakanin bangarorin biyu duk dai kan rikicin na Ukraine.

Sai dai shi Mr Putin din ya shaidawa BBC cewa sun zauna a teburi guda tare da Mr Peroshonko,kuma sun yi magana ta kusan minti 15, duk da yace ba cikakkiyar hira suka yi ba, amma sun tabo batutuwan da suke da alaka da yadda zaa kawo karshen halin da ake ciki da ci gaban tattalin arzikin kasashen biyu.