Mace ta kai harin kunar bakin wake a Gombe

Jami'an tsaro a Nijeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaro a Nijeriya

Rahotanni daga Gombe a arewa maso gabashin Nijeriya na cewa wata mace, 'yar-kunar bakin wake, ta kai harin bam a wani barikin soja, inda ta rasa ranta kana ta jikkata wasu sojoji.

Lamarin dai ya faru ne , da misalin karfe sha daya na safiyar Lahadi, a kusa da inda ofishin kwamandan bakirin soji na 301 yake( Quarter Guards).

Wasu jama'ar gari sun tabatar da jin karar fashewar wani abu a wurin.

Hukumomin 'yan sanda sun ce suna gudanar da bincike.

Amma wata majiyar soja ta tabbatar da aukuwar lamarin.