PDP ta yi amai ta lashe kan sabon Sarkin Kano

Image caption PDP tace ta ji kunya kan sanarwar Sabon Sarki

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria tayi amai ta lashe bayan data janye wata sanarwa data fitar tun farko wacce a cikinta take cewa tana taya Sabon sarki Chiroman Kano Alhaji Sanusi Ado Bayero murna.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Sakataren yada labarun jam'iyyar Oliseh Metuh ta ce sun sami labarin wata sanarwa da aka fitar da sunan sakataren PDPn wacce ke taya babban dan Sarkin murna Alhaji Sanusi Lamido Bayero a matsayin sabon sarki.

Sabuwar sanarwar tace Mr. Ihediwa wanda ya fitar da sanarwar taya murna tun farko a madadin Sakataren PDP ya dogara ne da wani labarin da ya ji daga wani gidan Talabijin dake nuna hakan, ba tare da ya samu amincewar Sakataren PDPn ba

Sanarwar tace wannan babban abin kunya ne ga jam'iyyar PDP mai mulki

Daga karshe sanarwar tace PDP na nisanta kanta daga waccar sanarwar ta farko wacce ke taya sabon Sarki Sanusi Ado Bayero murna