Tarihin Mallam Sanusi Lamido Sanusi

Image caption Gwamnatin Kano ta bada sanarwar nada Mallam Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sabon Sarki

An haifi Mallam Sanusi Lamido Sanusi a jahar Kano dake arewacin Nigeria a ranar 31 ga watan Yuli a shekarar 1961.

Ya samu digirinsa na farko a fannin tsimi da tanadi da kuma fannin shari'ar musulunci daga Jami'ar Amadu Bello dake zaria da kuma Jami'ar Khartoum dake Sudan.

Bayan ya koyar da tsimi da tanadi tsawon shekaru biyu a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, sai ya soma aikin banki a shekarar 1985 tare da Icon Limited, daga bisani kuma yai aiki tare da bankin UBA da kuma First Bank

Ya kai matsayin Babban Darakta a bankin First bank wanda shine banki mafi girma a Nigeria a watan Janairun shekarar 2009, daga bisani kuma aka nada shi gwamnan babban bankin Nigeria na 10 a watan Yunin shekarar 2009.

Sai dai Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya dakatar da shi daga matsayin Gwamnan a ranar 20 ga watan Fabrairun shekarar 2014 bayan da aka zarge shi da sakaci wajen harkar kudi

Kafin a dakatar da shi, Malam Sanusi ya yi zargin cewa Dala biliyan 20 sun bace daga cikin ribar da kamfanin man Nigeria wato NNPC ya samu

Mahaifinsa Muhammado Lamido Sanusi ya rike mukamin babban sakatare a ma'aikatar harkokin kasashen wajen Nigeria, bayan ya rike mukamin Jakadan Najeriyar a Kasashen Canada da Belgium da China.

Shine kuma jikan Sarkin Kano na 11 Alhaji Muhammadu Sanusi

Malam Sanusi Lamido Sanusi yana da iyali da kuma 'ya'ya.