An sace jirgin ruwan Liberia a Ghana

Wasu 'yan fashi a teku sun sace wani jirgin ruwa na kasar Liberia a gabar teku kasar Ghana a karshen mako.  Sashen hulda da jama'a na rundunar sojojin kasar Ghana ya ce yanzu haka sojojin ruwa na Ghana hade da takwarorinsu na Najeriya da Togo na gudanar da bincike don gano inda jirgin ya ke.  Rahotanni sun ce matukin jirgin ne ya bayyana cewa 'yan fashi sun kai musu hari.  Matsalar fashi a teku dai na ci gaba da kamari musamman a yankunan da ke gabar teku Guinea inda 'yan fashi ke sace jiragen ruwa tare da yin garkuwa da mutane. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin ruwan Italiya da 'yan fashi suka sace a gabar tekun Guinea a shekarar 2011

Wasu 'yan fashin teku sun sace wani jirgin ruwa na kasar Liberia, a gabar tekun kasar Ghana a karshen mako.

Sashen hulda da jama'a na rundunar sojin Ghana ya ce yanzu haka sojojin ruwa na kasar da takwarorinsu na Najeriya da Togo na gudanar da bincike don gano inda jirgin ya ke.

Rahotanni sun ce matukin jirgin ne ya sanar da cewa 'yan fashi sun kai musu hari.

Matsalar fashin teku dai ta yi kamari a yankunan da ke gabar tekun Guinea, inda a lokuta da dama ake sace jiragen ruwa tare da yin garkuwa da mutane.