Rikici ya sake barkewa a Karachi

Sojojin Pakistan a filin jirgin sama na Karachi Hakkin mallakar hoto AFP GETTY
Image caption Kungiyar Taliban ita ce ta dauki nauyin kai harin.

Sabon rikici ya barke a filin jiragen sama na kasa da kasa da ke birnin Karachi a Pakistan, sa'o'i bayan da hukumomi suka sanar da cewa komai ya lafa bayan musayar wutar da suka yi da wasu 'yan bindiga da akalla mutane ashirin da uku suka rasa rayukansu ciki har da maharan su 10.

Wannan Pasinjan da ya sauka a filin jirgin gabannin harin ya shaidawa BBC cewa

Yace ba su dade da sauka ba daga birnin Lahore, su na shiga dakin da pasinjoji ke daukar jakunkunan su aka fara tashin hankalin.

Sun kuma ji karar ababen fashewa nan da nan kuma jami'an tsaro suka rufe kofofi kana suka ce kowa ya ci gaba da kasancewa a inda ya ke.

Kungiyar Taliban ta dauki nauyin kai harin, kungiyar da a baya ma ta sha kai hare-haren kan sansanonin jami'an tsaro a kasar ta Pakista.