An yi taron yaki da bauta a Nijar

Shugaban kasar Nijar Muhammadou Issoufou Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matsalar bauta dai ta yi kamari a wasu sassa na jamhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijar kungiyar Timidria mai yaki da bauta a kasar ta shirya wani taro tare da hadin gwiwar hukumomin yaki da bauta da ma safarar bil'adama domin tattaunawa a kan matsalar bauta a yankin kasashen afrika ta yamma.

Duk da cewa babu alkaluma tabbatattu,rahotanni na nuni da matsalar bautar na da girma a yankin na afrika ta yamma.

Timidria ta shirya taron ne albarkacin ranar yaki da bauta a afrika ta yamma da kasashen yankin ke rayawa yau din nan.