Rahoto kan makarantar Musulmai a Birtaniya

Image caption Ana sauraron martani daga hukumomin wannan makarantar

Wani rahoton hukumar sa'ido kan Ilimi a Birtaniya watau Ofsted ya ce wata makarantar musulmai ba ta taimaka wa wajen 'koyar da hakuri' sannan akwai wasu littatafai a makarantar da ke nuna alamun jefewa ko yin bulala a matsayin hanyar ladabtarwa.

Masu bincike sun ce wasu littatafai a dakin karatu a makarantar na kunshe da wasu ra'ayoyi masu tsauri da hukunce-hukuncen da "basu da mazauni a al'ummar Birtaniya".

Hukumar binciken kan ilimi ta ce makarantar Faramare ta Olive Tree da ke kan titin Bury Park a Luton "ba ta cike wasu ka'idoji ba" sakamakon ziyarar binciken da aka gudanar da watan Mayu.

Kawo yanzu makarantar ba ta maida martani ba, amma ta bukaci a masu bincike su sake gudanar da bincikensu.

An dakatar binciken da aka shirya gudanarwa a watan da ya wuce saboda wasu iyaye sun yi korafi a kan cewar an yi wa 'ya'yansu tambayoyi game da luwadi da madigo.

'Hujja'

Hukumar binciken ta ce a yanzu haka ta samu "hujjoji masu yawa" don rubuta rahotonta.

Image caption Makarantar Musulmai a Luton

Masu sa'ido din sun ce "ba a baiwa yara dama sosai wajen mu'amala da wasu al'adu da addinnai domin su kasance masu hakuri da juriyya tare da kuma sannin al'adun wasu al'ummomin".

Rahoton ya kara da cewar shugabannin makarantar ba sa tabbatar da "samun bayanai ma daidaita a kan duniya" sannan kuma wasu littatafan da ke makarantar na goyon bayan jefewa da kuma yin bulala a matsayin hanyoyin ladabtarwa.

A cewar rahoton akwai karancin littatafai a kan sauran addinnan duniya baya ga Musulunci.

Bugu da kari, rahoton ya ce ba a koyar da dalibai yadda ya dace domin samun ci gaban da suke bukata.

Amma dai rahoton ya ce dalibai da ke aji 6 sun kai "matsayin da ya sace" a karatu, sannan koyarwar Larabci ya taimaka wajen 'tarbiyar' daliban.

Ana bukatar makarantar ta dauki mataki domin cimma ka'idar da aka saka kan makarantu masu zaman kansu.

Watau koyar da dalibai abubuwan da "za su taimaka musu wajen zama a wannan zamanin a Birtaniya" da suka yi daidai da "dokar kasa".

Shugaban makarantar, Farasat Latif a baya ya ce za su dauki matakin shari'a idan ba a gudanar da sabon rahoto ba.