Jaridu: An nemi a ja kunnen Nigeria

Wani na karanta jaridar
Image caption Gidajen jaridun sun ce sojojin sun kuma yiwa masu sayar da jaridun tambayoyi, sannan sun kona wasu jaridun

Kungiyar kare hakkin bil'Adama ta SERAP a Najeriya ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da Gwamnatin Goodluck Jonathan daga cin zarafin gidajen jarida.

A ranakun Juma'a da Asabar da suka wuce ne sojoji suka kai samame kan jaridun Leadership da Punch da Daily Trust da The Nation da kuma Vanguard.

Dakarun sun kai samame a wuraren da ake rarraba jaridu a kasar, suka kuma bincika motocin daukar kaya da ke jigilar jaridun.

Sai dai jami'an tsaro sun ce suna aikinsu ne kawai na tabbatar da tsaro, kana sun musanta cewa sun kwace wasu jaridun.

Hakan na zuwa ne yayin da Shugaba Jonathan ke fuskantar matsin lamba domin ya kara kaimi wajen magance matsalar Boko Haram da ta addabi arewacin kasar.