An kashe sojojin Amurka a Afghanistan

Dakarun Amurka a Afghanistan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin kungiyar NATO na ci gaba da fafutika a Afghanistan

Dakarun sojin Amurka sun hallaka wasu takwarorinsu bisa kuskure a kudancin Afghanistan.

Wata majiyar soji ta ce lamarin ya faru ne ranar Litinin lokacin da dakarun Amurka da na Afghanistan ke aikin hadin guiwa a lardin Arghandab da ke Zabul a kokarinsu na fatattakar 'yan Taliban.

Wasu jami'an Afghanistan sun ce an hallaka sojojin Amurka biyar ne da kuma wasu sojojin Afghanistan biyu lokacin da jirgin yakin Amurka ya kai hare-hare a lardin.

Rahotanni sun ce fiye da sojojin kungiyar kawance ta NATO 30 ne suka halaka a Afghanistan a wannan shekarar.