" 'Yan Boko Haram za su dandana kudarsu"

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan matan Chibok da aka sace

Wakiliyar musamman ta majalisar dinkin duniya game da batun yin fyade a lokacin yaki, Zainab Bangura ta ce, masu hannu a satar, mata a yankin arewa maso gabashin Nigeria, za su dandana kudarsu.

Zainab Bangura tana magana ne, bayan da aka sami labarin satar wasu mata akalla ashirin, daga wata rugar Fulani a jahar Borno, kusa da garin Chibok - watau inda 'yan Boko Haram suka sace 'yan matan sakandare fiye da dari biyu da hamsin, kusan watanni biyu kenan.

A cewarta wannan muguwar tabi'a dai ba a Afirka ta tsaya ba.

Alal misali, a lokacin yakin Yugoslavia na farkon shekarun 1990, mata kimanin dubu sittin ne aka yi wa fyade, in ji wani kiyasi na majalisar dinkin duniya.

Haka ma a Syria mutane fiye da dubu talatin da takwas sun nemi taimakon majalisar a bara, bayan an ci zarafinsu.

Zainab Bangura ta ce, duk masu aikata mugayen laifufuka a kan mata, ba za a barsu su tafi salin-alin ba.

Karin bayani