Jirgin yakin Faransa ya fadi a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Faransa na amfani da jiragen yaki shida a Mali

Jirgin saman yakin Faransa mai suna Mirage 2000D da ake amfani da shi a Mali ya fadi a cikin hamadar Jamhuriyar Nijar.

Kakakin sojin Faransa, ya bayyana cewar jirgin ya samu 'yar tangarda ne amma kuma matukansa biyu sun tsira ba tare da rauni ba.

Gilles Jaron ya kara da cewar jirgin saman yakin yana kan hanyarsa ta dawowa daga Mali ne sai ya fadi a tsakanin Gao da kuma birnin Niamey inda sansanin sojin Nijar suke.

Jirgin yakin mai tsadar gaske, na daga cikin jiragen yaki shida da dakarun Faransa ke amfani dasu a yankin da ake fama da rikici da 'yan tawayen Mali.

A cikin watan Junairun 2013, Faransa ta tura dakarunta zuwa Mali don yaki da 'yan tawayen da suka kwace arewacin kasar.

Faransa na da dakarun kusan 1,600 a yankin.

Karin bayani