Jirgin ruwa ya kife da masunta a Ghana

Taswirar kasar Ghana
Image caption Ana ci gaba da aiki don gano kwale kwalen da sauran masuntan

Rahotanni daga kasar Ghana sun ce akalla masunta 8 ne ake fargabar sun mutu, bayan wani kwale-kwalen da su ke tafiya a ciki ya kife a teku.

Masuntan su 20 sun taso ne daga garin Sekondi da ke yammacin kasar a ranar Talata don zuwa birnin Tema mai tashar jiragen ruwa, don a gyara kwale-kwalen da suke kamun kifi da shi.

An samu ceto masunta 12 yayin da kuma aka tura wasu sojojin ruwan kasar cikin ma'aikatan ceto don gano kwale-kwalen da sauran masuntan.

Rahotanni sun ce wata igiyar ruwa mai karfi ce ta fizge kwale-kwalen lamarin da ya yi sanadiyyar kifewarsa.