An tube sarakuna 2 a jihar Imo

Gwamnan jihar Imo a Najeriya Rochas Okorocha Hakkin mallakar hoto no
Image caption Gwamnan jihar Imo a Najeriya Rochas Okorocha

A Najeriya gwamnan jihar Imo, Cif Rochas Okorocha ya bayar da sanarwar tube sarakunan gargajiya 2 a bisa zargin aikata ba daidai ba.

Sarakunan gargajiyan biyu dai sune Eze Cletus Ilomuwanya na garin Obinugu a yankin karamar hukumar Onu da kuma Eze Cosmos Onyenike na garin Lagwa Opkato.

Kwamishina yada labarai na jihar ta Imo ya ce, an sauke su ne saboda ana zarginsu da aikata abubuwan da bai kamata duk wani basarake ya aikata ba.

To sai dai sarakunan sun yi watsi da wannan mataki da gwamnatin ta dauka, kuma sun ce ba shi da wani tasiri, domin ba a aiwatar da shi bisa doka ba.