Amurka ta kama Abu Khatallah a Libya

Tambarin hukumar bincike ta FBI Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tambarin hukumar bincike ta FBI

Amirka ta kama daya daga cikin jagororin da ake zargi da kai hari akan ofishin jakadancinta dake Benghazi na kasar Libya a shekarar 2012.

Shugaba Obama yace dan bindigar Ahmed Abu Khatallah zai fuskanci cikakken hukunci bisa tsarin shari'ar Amirka.

Sojojin Amirka ne wadanda ke aiki tare da hukumar tsaro ta FBI suka cafke shi a kusa da Benghazi a ranar Lahadi.

A yanzu Amirka na tsare da shi a wani wuri a wajen Libya kuma za'a tasa keyarsa zuwa Amirkan domin fuskantar shari'a.

A lokacin tarzomar da aka yi a Benghazi shekaru biyu da suka Amirkawa hudu sun rasa rayukansu ciki har da jakadan Amirkar a Libyan Chris Stevens.