An kashe 'yan tawaye 100 a Sudan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan tawayen Sudan na fafatawa da gwamnati a Kordofan

Sojan Sudan sun ce, sun kashe 'yan tawaye fiye da dari a jihar kudancin Kordofan.

Kakakin sojan Sudan , Sawarmi Khaled Sa'ad ya ce, an kashe 'yan tawayen ne yayin gurmurzun sa'o'i uku a kokarin dakile harin 'yan tawayen a kan yankin El Atmor.

'Yan tawayen na kungiyar SPLM ta arewa sun tabbatar da kai harin, amma suka ce, dakarunsu uku ne kawai aka kashe.

Kungiyar 'yan tawayen ta shafe shekaru biyu tana yakar gwamnatin Sudan a wannan yankin.

Majalisar dinkin duniya ta ce, mutane fiye da miliyan guda ne lamarin ya shafa.

Karin bayani