'Fyade abin kunya ne ga masu aikata shi'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Angelina Jolie da Sakataren harkokin wajen Burtaniya William Heague ne suka karbi bakuncin taron na London

Tauraruwar fim din nan kuma wakiliya ta musamman ta Majalisar Dinkin Duniya, Angelina Jolie ta ce dole taron kolin da ake yi a London ya aike da sako ga wadanda suka fuskanci cin zarafin cewa ba sa cikin halin kaskanci.

Ms. Jolie ta ce akwai bukatar duniya ta fahimci cewa abin kunyar na tattare ne da wadanda suka aikata cin zarafin.

An dai kwashe shekaru biyu ana kamfe game da batun kawo karshen cin zarafin mata a lokutan yaki a duniya.

Kuma kamfe din ya zaga kasashen duniya 148 wadanda suka amince su dauki mataki domin kawo karshen matsalar.