Boko Haram: A ba mutane damar daukar makamai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan Civilian JTF a Maiduguri

Wasu shugabannin al'umma a Nigeria sun soma yin kira a baiwa jama'a izinin daukar makamai don kare kansu, a yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da hare-haren 'yan Boko Haram.

Hakan na faruwa yayin da ake cigaba da kashe daruruwan jama'a a wannan yanki, sannan kuma dubban jama'a na tserewa daga can.

Shugaban al'ummar Chibok mazauna Abuja, Dr Pogu Bitrus a hirarsa da BBC ya ce tunda sojoji sun kasa, to kamata yayi a ba 'yan banga izinin daukar makaman.

Bitrus ya ce "Gwamnati ta bada izinin daukar makamai saboda sojoji ba sa kare mutane".

A cewar Dr Bitrus hakan zai sa a kaucewa fadawa cikin rikicin addinnin a kasar.

Kungiyar Boko Haram mai cibiyarta a jihar Borno ta kashe mutane fiye da 3,300 a wannan shekarar sannan kuma ta sace dalibai 'yan mata fiye da 200 a wata makaranta a Chibok.

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya ce ba za su saki 'yan matan ba har sai an sako 'yan Boko Haram da ake tsare da su a gidajen yari a Nigeria.

Karin bayani