Facebook ya yi kuskuren fitar da Slingshot

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dandalin Facebook na da farin jini a duniya

Dandalin sada zumunta da bayyana ra'ayoyi na Facebook ya fitar da wata sabuwar manhajar aika sakonni hotona bisa kuskure ta hanyar kanti saida kayayyakin kamfanin Apple.

Sabuwar Manhajar mai suna 'slingshot' ta kunshi abubuwa da suka hada da rarraba hotona da hoton bidiyo tsakanin abokai da aika ra'ayi ta hanyar amfani da hoto.

A manhajar Snapchat, a na goge hotona da zarar an aika sakon haka kuma masu amfani da ita na iya yin rubutu a kan hotonan.

Kamfanin Facebook ya tabbatar da wanzuwar manhajar ta "Slingshot" sai dai ba bu tabbabacin ranar da za a kaddamar da ita.

Wakilai daga 'The Verge da TechCrunch' sun dauki hoton da ke kan Allo na tallar manhajar kafin Facebook ya janye ta.

Hotonan da suka bayyana, sun nuna abubuwa da dama musamman wadanda ba a saba ganin irin su ba da suka hada da kimiyar budewa ta inda hoton da aka karba daga hannun aboki za a iya sake aika shi ga wanda ya turo.

Sai dai an ji cewa an sanya wa sabuwar manhajar suna 'slingshot' ne saboda zuwa da dawowar sakonnin hotonan.

Facebook ya tabbatar da sanarwar cewa, "tun da fari , ya saki sabuwar Manhajar ta Slingshot' ba da gangan ba, sabuwar Manhaja ce da muke aiki kanta."

Kamfanin bai bayyana lokacin da za a fara sai da Manhajar ba inda ya ce "za a kammala ta nan gaba kadan, muna kuma fatan za ku jarraba ta."

Karin bayani