Mutane rabin miliyan sun tsere daga Mosul

Masu gwagwarmaya da makamai a Iraqi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu gwagwarmaya da makamai a Iraqi

Rahotanni daga Iraqi sun ce kimanin mutane rabin miliyan ne suka tsere daga Mosul wanda ya fada hannun 'yan gwagwarmaya a ranar talata.

'Yan gwagwarmaya masu kishin Islama na ci gaba da mamaye wasu sassan kasar abinda Amurka ta bayyana a matsayin wata babbar barazana ga daukacin yankin.

'Yan Sandan Iraqin sun bayyana cewar 'yan gwagwarmayar masu yunkurin kafa kasar Iraqi mai bin tafarkin Islama watau ISIS a takaice, sun kuma kwace garuruwa da birane a lardunan Kirkuk da Salaheddin.

Amurka dai ta yi kira ga Prime Ministan Nouri al Maliki wanda dan Shi'a ne da ya yi kokari tare da tsirarru 'yan Sunni domin farfado da doka a yankin.

A wani taron manema labarai a birnin Washington, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki ta ce, tillas 'yan kasar ta Iraqi su hada kai su yaki abinda ta kira barazanar da ake kara samu ta masu gwagwarmaya da makamai.

Karin bayani