Sabon Sarkin Kano bai shiga fadarsa ba

Image caption Tun a ranar Litinin sabon sarki a karbi takardar soma aiki

Kwanaki uku bayan nada sabon Sarki a masarautar Kano, har yanzu sabon sarkin bai shiga cikin gidan sarauta ba.

Tun a ranar Lahadi, gwamnatin jihar Kano ta nada Malam Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sabon sarki sannan kuma aka rantsar da shi a ranar Litinin.

Sabon sarkin mai martaba, Malam Sanusi Lamido Sanusi har yanzu yana zaune ne a fadar gwamnatin jihar Kano inda a nan yake karbar gaisuwa.

Hakimai da sauran al'umma na ci gaba da mubaya'a ga sabon sarkin a cikin fadar gwamnatin jihar Kano.

A gidan Sarautar dai ana ci gaba da gudanar da zaman fada na al'ada da karbar gaisuwa, da kade kade har ma da bushe-bushe.

Bayanai sun nuna cewar an girke jami'an tsaro a kewayen gidan Sarkin Kano, abinda ya sa wasu ke ganin cewar hakan ne ya hana sabon sarkin shiga cikin fadar sa.

A ranar Juma'ar da ta wuce ne tsohon sarki, Alhaji Ado Bayero bayan shafe fiye da shekaru 50 a kan mulki.