Rudani a majalisar dokokin jihar Edo

Gwamnan jihar Edo a Najeriya Adams Oshiomole Hakkin mallakar hoto edo govt
Image caption Gwamnan jihar Edo a Najeriya Adams Oshiomole

A Najeriya, ana rudani majalisar dokokin jihar Edo, bayan mataimakin shugaban majalisar da aka ce an dakatar ya jagoranci tattaunawa da wasu 'yan majalisar.

Mataimakin shugaban majalisar da wasu 'yan majlisar dai sun yi wani kwarya-kwaryar zama a zauren majalisar, inda su ma suka ce sun dakatar da kakakin da wasu 'yan majalisar su shida.

To, sai dai shugaban majalisar dokokin ya yi watsi da wannan mataki, wanda yace wasu 'yan tsiraru ne maras sa tasiri suka ayyana.:

Bayanai sun ce lamarin ya abku ne bayan da mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Edo ya jagoranci wasu 'yan majalisar da aka ce an dakata tare da shi bayan sun yi sauyin sheka daga jam'iyar APC mai mulkin jihar zuwa jam'iyar PDP.

Majalisar dokokin ta fada cikin dambarwar ne sakamakon isa zauren majalisar da shugaban majalisar da sauran 'yan majalisar suka yi, suna mai ikirarin sune mafi rinjaye.