An kashe mutane 10 a Riyom na Filato

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Jihar Filato ta saba fuskantar rikicin addinni

Wani sabon rikici ya barke a karamar hukumar Riyom ta jihar Filato a Nigeria inda aka kashe akalla mutane goma kuma aka kona gidaje da majami'a, tare da kashe shanu masu yawan gaske.

Lamarin ya faru ne a kauyukan Jol da Tanjo da ke yankin Riyom, inda Fulani da 'yan kabilar Berom ke zargin juna da haddasa rikici.

Tun a ranar Litinin da ta gabata ne aka shiga zaman dardar a Riyom, bayan wani hari da aka kai kan Fulani makiyaya kuma aka kashe shanu da dama, lamarin da ya kara ta'azzara daga daren Talata zuwa wayewar garin laraba.

Shugaban matasan kabilar Berom, Mista Rwang Dalyop Dantong, ya shaidawa BBC cewa wasu mahara da ake zargin Fulani ne sun kai hari a daren jiya (Talata) zuwa wayewar yau (Laraba), a kauyen Tanjol inda suka kona gine-gine da dama, kuma suka kashe 'yan kabilar Berom biyar da sojoji biyar bayan sun yi musayar wuta.

Sai dai Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah a jihar ta Filato, Alhaji Haruna Boro Husseini, ya musanta hannun Fulani a harin na Riyom, amma ya ce abin da ya sani shi ne 'yan kabilar Berom sun kashe shanun Fulani da dama kuma sun sace wasu bayan jikkata wasu makiyaya a ranar Litinin.

Karin bayani