Jam'iyyar APC na babban taro a Abuja

Jam'iyyar adawa ta APC
Image caption APC na fama da rigingimun cikin gida a wasu jihohin Nigeria

Babbar Jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria na gudanar da babban taron ta na kasa a Abuja domin zaben shugabanninta.

Jam'iyyar APC dai na fama da rigingimu na cikin gida a wasu jihohin kasar sakamakon zaben shugabannin a matakan kananan hukumomi da na jihohin, lamarin da ya janyo baraka a tsakanin 'ya'yanta.

An kuma tsaurara matakan tsaro inda kimanin wakilai dubu bakwai za su halarci taron da za a yi a Abuja babban birnin tarayya.

Wannan shi ne karon farko da jam'iyyar ke babban taro na kasa don zaben shugabanninta tun bayan da ta hade da sauran jam'iyun adawa a kasar.