Neman halatta shan tabar wiwi a Afrika

Ganyen tabar wiwi
Image caption Yankin yammacin Afrika ne ke kan gaba wajen shan tabar wiwi a duniya

Wani kwamitin da ya kunshi manyan wakilai na kasashen yammacin Afrika sun nemi da a janye dokokin da suka haramta shan tabar wiwi a kasashen da ke yankin.

A rahoton da kwamitin ya fitar karkashin jagorancin tsohon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan da tsohon shugaban Nigeria Cif Olusegun Obasanjo, ya ce babu wata nasara da ake samu wajen hukunta masu shan tabar wiwi.

Kwamitin ya kara da cewa babu abin da haramta shan tabar wiwi ya haifar sai cunkoso a gidajen yari tare da karfafa matsalar cin hanci da rashawa a tsakanin jami'an 'yan sanda da na bangaren shari'a, a kasashen yankin.

Rahotanni sun ce yankin yammacin Afrika ne ke kan gaba wajen shan tabar wiwi a duniya.

A wata kididdiga da ofishin kula da shan miyagun kwayoyi ta majalisar dinkin duniya da fitar , ya nuna cewa adadin matasan da ke taammali da wadannan kwayoyi a yammaci da Afirka ta tsakiya ya kai kashi 12.4 cikin 100 idan aka kwatanta shi da matsakaicin adadin kashi 7.5 a Afirka da kuma kashi 3.9 a duniya baki daya.

Yawancin kasashen yammacin Afirka na da tsauraran dokoki kan aikata laifin shan miyagun kwayoyi inda a wasu lokutan a ke yanke wa ma su iri wadannan laifi hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekaru 10- zuwa 15 sakamakon samun su da mallakar irin kayan mayen.