Giwaye na karewa a Afrika

Giwaye a Afrika Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Adadin giwayen da ake haifa a Afrika na raguwa

Wata hukuma ta kasa da kasa da ke kokarin kare dabbobin da ke karewa a duniya ta ce giwaye a Afrika na fuskanta barazanar karewa matukar aka ci gaba da farautar haurensu a nahiyar.

A wani rahoto da ta fitar, hukumar ta ce a kowace shekara ana hallaka giwaye dubu 20 a kasashen Afrika.

Wannan adadi ya zarta yawan giwayen da ake haifa a nahiyar.

Rahoton ya kuma nuna karuwar hauren giwa da hukumomi ke kwacewa a Afrika, lamarin da ya nuna cewa fasakwaurin hauren giwa wata harka ce da ta kunshi wasu gungun mutane a kasashen duniya.