An rufe gidajen kallon kwallo a Filato

Masu kallon kwallon kafa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu mutane sun hallaka a harin bama-bamai da aka kai a gidajen kallon kwallon kafa

Rundunar 'yan sanda a jihar Filato da ke Nigeria ta haramta bude gidajen kallon kwallo a jihar, har sai bayan an kammala gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.

Rundunar 'yan sandan ta ce ta dauki wannan mataki ne saboda hare-haren da ake kai wa a wasu gidajen kallon da ke jihar.

A kwanakin bayan ne dai aka hallaka wasu mutane a hare-haren bama-bamai da aka kai a gidajen kallon kwallo a jihar.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da mahukunta a jihohin Adamawa da Yobe suka ba da sanarwar rufe gidajen kallon kwallon a jihohinsu, har sai an kammala gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka fara a Brazil.