An kasa kafa dokar ta baci a Iraki

Shugaban Majalisar dokokin Iraki Osama Al Nujaifi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan majalisar dokokin basu isa a gudanar da kuri'ar ba

Majalisar dokokin Iraki ta gaza kada kuria domin amincewa da wani kuduri da zai ayyana dokar ta baci yayin da masu fafutikar Islama na kungiyar ISIS, suka lashin takobin ci gaba da dannawa zuwa Bagadaza, babban birnin kasar.

Adadin 'yan majalisar da suka je zauren majalisar dai bai isa a gudanar da kuri'ar ba, wadda Fira Minista Nuri Al Maliki ya bukaci a gudanar.

A bangare guda kuma kasar Turkiyya ta ce tana iya bakin kokarinta na ganin an sako 'yan kasar ta su 80 da aka kama a birnin Mosul na Iraki.

A ranar Talata ne dai kungiyar masu fafutikar Islama ta ISIS mai alaka da al Qaida ta cafke wasu direbobin manyan motoci su 31 'yan Turkiyya, sannan kuma ta kama wasu ma'aikatan karamin ofishin Jakadancin Turkiyyar a Mosul su 49 a ranar laraba.

Ministan harkokin cikin gidan Turkiyyar, Efkan Ala, ya ce ma'aikatan karamin ofishin jakadancin na cikin koshin lafiya, kuma ya ce yana fatan za a sako dukkan mutanen da aka sace.

A ranar Laraba ne dai Turkiyyar ta yi gargadin cewa za ta dauki matakai na ramuwar gayya, idan har aka cutar da wani daga cikin 'yan kasar ta.