Oyegun ne sabon shugaban jam'iyyar APC

Image caption An gudanar na da taron wanda ya gudana har talatainin daren ranar jumu'a ne a dandalin Eagles Square da ke Abuja.

Mr. John Oyegun tsohon gwamnan jihar Edo da ke kudancin Najeriya ne aka zaba babu hamayya a zaman sabon shugaban jam'iyyar adawa mafi girma a kasar.

Mr. Oyegun ya zamo shugaban jam'iyyar ne bayan da babban abokin karawarsa takarar shugabancin jam'iyyar kana tsohon gwamna jihar Bayelsa ya ce ya janye daga takarar a yayin babban taron jam'iyyar na farko a Abuja ranar jumu'a.

''Dukkanku kun sani cewa na tsaya takarar shugabancin wannan jam'iyya. Sai dai muradina ba na na in yi nasara ni kai da ba ne, shi ne na nasarar wannan babbar jam'iyyar da kuma ci gaba da dorewar ta. Don haka na janye kuma na mara wa Mr. John Odigo Oyegun baya,''Inji Shi.

Wasu majiyoyi dai sun ce janyewar Mr. Sylva daga takarar na da nasaba da wata ganawar sa'aoi da aka yi tsakanin dattawan jam'iyyar karkashin jagorancin chief Bola Tinubu da ke goyon bayan Mr. Oyegun da kuma gwamnonin jam'iyyar da ke goyon bayan tsohon takwaran aikin nasu a jihar Bayelsa.

Sauran shugabanni

Ta irin haka ne kuma aka zabi Maimala Buni daga jihar Yobe a zaman Sakataren kasa na Jam'iyyar domin ya maye gurbin Sakateren riko Tijjani Tumsah.

Maimala Buni ya zamo sakataren jam'iyyar shi ma babu hamayya bayan wata sanarwa da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar yayi cewa dattawan jam'iyyar daga shiyar arewa-maso-gabas sun shawo kan abokin karawarsa Kashim Imam ya janye masa.

An zabi tsohon gwamnan jihar Ekiti Segun Oni wanda ya shigo jam'iyyar daga PDP a watan jiya a zaman mataimakin shugaban jam'iyyar na yankin kudu yayinda aka zabi Sakataren rusasshiyar jam'iyyar ACN Lawan Shuaibu a zaman sakataren jam'iyyar na yankin arewa.

An sake zaben sakataren watsa labaran jam'iyar na riko Mr. Lai Mohammed a zaman sakataren na watsa labarai.

Wadannan shugabannin dai da wasu da dama da aka zabe a daren jiya, su ne za su jagoranci jam'iyyar a manyan zabubukan shekara mai zuwa.

Karin bayani