Sojojin Iraqi na kokarin kwato Samarra

Mayakan kungiyar ISIS Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption ISIS dai ta dade ta na kai hare-hare a wasu sassa daban-daban na kasar Iraqi.

Sojoji masu biyayya ga gwamnatin Iraqi sun bazu a sassa garin Samarra don yakar masu tada kayar baya da suka kwace iko da wasu sassan yammaci da kudancin kasar.

Suma Dakarun sojin gwamnati tare da sojojin sa kai sun shiga cikinsu bayan Prime Ministan kasar Nouri Al-Maliki da shugaban 'yan Shia Ayatollah Ali al-sistani sun ba su umarnin yin hakan.

Rahotanni sun bayyana cewa Dr Maliki ya kai ziyara garin Samarra mai nisan kilomita dari daga arewacin babban birnin kasar Bagadaza.

Wasu rahotannin na kara cewa wani janal na sojin kasar Iran ya isa Bagadaza, duk da cewa Tehran ta musanta cewa ta na da karfin fada aji da makotanta.

Shima shugaba Obama ya yi alkawarin daukar kwakkawarn mataki akan masu tada kayar bayan da yace ba wai Iraqi da al'umar cikin ta kadai suke yi wa barazana ba har ma da Amurka kan ta.