Mutane 22 ne suka mutu a kauyen Dagu

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa JTF a jahar Borno Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ba wannan ne karo na farko da 'yan bindiga ke kai hari kauyukan jihar ta Borno ba.

A Nigeria, adadin wadanda suka rasa rayukansu a harin da 'yan bindiga suka kai a kauyen Dagu da ke jihar Borno ya karu zuwa 22.

Rahotanni na kuma nuna cewa jama'a na barin kauyen, sakamakon harin da wasu da ake zargin 'yan Boko haram ne suka kai a ranar Lahadi.

'Yan bindigar sun kai harin ne a lokacin da kasuwar Shanu ta kauyen ke ci, kana sun kona wani coci tare da sace ababen hawa da dama.

Wani dan majalisa da mazabarsa ke makwabtaka da yankin, Tisfi Ganama ya tabbatar da afkuwar lamarin.