Sojojin Iraki na gwabzawa da Mayakan ISIS

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashen Yamma dai sun dora laifin barkewar fadan a Iraki ga manufofin nuna wariya na Farayin Minista Al-maliki.

Rahotanni daga Iraki na cewa dakarun gwamnati da mayakan sa-kai 'yan shi'a na kokarin mai da mayakan sa-kai 'yan sunni wadanda ke kokarin dannawa zuwa cikin birnin Bagdaza baya.

Sojojin na Iraki da mayakan na sakai 'yan shia dai sun samu nasarar sake kwato wasu garuruwa daga hannun 'yan tawayen.

Sai dai har yanzu muhimman biranen Tikrit da Mosul na ci gaba da zama hannn 'yan takifen.

A wata a rangama da aka yi a arewa maso gabas ga birnin na Baghdaza wani jirgi mai saukar ungulu na gwamnati ya kai hari inda ya kashe wasu mayakan kurdawa 7; kodayake jami'an irakin sun ce harin kuskure ne.

Karin bayani