An kashe mutane 50 a Jihar Taraba

Hakkin mallakar hoto AP

Rahotanni daga Jihar Taraba a Najeriya sunce mutane kusan 50 ne aka kashe wasu fiye da 100 kuma suka jikkita a wani sabon tashin hakali da ya barke ranar Lahadi a Karamar Hukumar Wukari.

Rikicin, mai nasaba da addini da kabilanci, ya bazu zuwa yankin Ibi.

Shugaban matasan Hausawa da Fulani a Wukarin, Malam Audu Ali, ya sheda wa Sashen Hausa na BBC cewa a gabansa motocin hukumomi da na agaji suka kwashe wadanda lamarin ya rutsa dasu.

Shima shugaban matasan kabilar Jukun a Wukarin, Mista Zondo Hoku, ya gaya wa BBC cewa an yi asarar rayuka da dukiya a rikicin.

Rikicin ya bazu zuwa Karamar Hukumar Ibi musamman cikin garin Ibi, inda nan ma aka samu asarar rayuka da na kaddarorin jama'a.

Kakakin rundunar 'yan sandan a Jihar ta Taraba, DSP Joseph Kwaji, yace rikicin ya lafa.

Tashin hankalin na Wukari dai ya soma ne da sanyin safiyar Lahadi lokacin da Hausawa suka zargi Jukunawa da kona wasu shaguna biyu na Hausawa -- zargin da Jukunawa suka musanta.

Abin dai ya kai ga cacar-baki tsakanin bangarorin biyu daga nan kuma rigimar ta'azzara, har ta kai ga kashe kashe.

Karin bayani