Bikin ranar yara ta Afrika

Bukin ranar yara ta Afrika Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana gudanar da bukukuwa don tunawa da ranar yara ta Afrika

Ranar 16 ga watan Yunin kowace shekara ce ake bikin ranar yara ta Afrika, domin tunawa da wasu ‘yan makaranta da aka hallaka a unguwar marasa galihu ta Soweto, a Afirka ta Kudu.

A rana mai kamar ta yau ce a shekarar 1976 dubban ‘yan makaranta bakaken fata suka famtsama kan tituna domin zanga-zanga game da wariyar da ake nuna musu ta bangaren ilimi.

Haka kuma daliban sun nemi a tabbatar da ‘yancinsu na koyar da su da harsunansu na asali.

An hallaka daruruwan daliban tare da raunata wasu da dama a makonni biyu da aka kwashe ana zanga-zangar a wancan lokacin.