An kafa dokar hana auren dole a Burtaniya

Firai ministan Burtaniya, David Cameron a tsakiya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan matan da ake yi wa uaren dole ba sa wuce shekaru 15

Wata sabuwar doka da ta hana auren dole ta soma aiki a Burtaniya da kuma yankin Wales.

A karkashin dokar aikata auren dole ya zama wani babban laifi, kuma duk wanda aka kama za a yanke masa hukuncin shekaru bakwai a gidan kaso.

Ana tunanin cewa dubban 'yan mata 'yan asalin kudancin nahiyar Asia ne ake yi wa auren tilas duk shekara a Burtaniya da Wales.

Masu fafutukar yaki da auren dole sun yi maraba da dokar, yayin da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan kasar ya ce dokar ta saukaka aikinsu, domin ta tantance menene auren dole.