Masu fafutuka a Iraqi sun karbe iko da Tal Afar

Wasu masu dauke da makamai
Image caption Majalisar dokokin Iraqi ta gagara ayyan dokar ta-baci

Masu tsattsauran ra'ayin Islama na kungiyar ISIS, tare da sauran kungiyoyin Sunni masu dauke da makamai, sun sake kama wani garin a Iraqi.

Garin Tal Afar da ke arewa maso yammacin kasar, ya fada a hannun 'yan gwagwarmayar ne bayan an gwabza kazamin fada.

Sojoji da 'yan sanda sun zubar da makamansu sun ranta a na-kare, sai dai gwamnatin Iraqi ta ce ana ci gaba da fafatawa domin karbe iko da Tal Afar.

A halin yanzu masu fafutukar sun kama manyan birane biyu da garuruwa uku a Iraqi, tun lokacin da suka kaddamar da farmaki mai kama da guguwa a farkon wannan watan.

Karin bayani