An hallaka mutane 48 a Kenya

Image caption Mutane a yankin na fargabar sa ke kawo musu wani hari

Jami'an 'yan sanda a Kenya sun ce wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Al-Shabab ne sun hallaka akalla mutane 48 a wani gari da ke kusa da gabar teku a tsibirin Lamu.

Rahotanni sun ce 'yan bindigan sun kwace wasu manyan motoci guda biyu suka kuma umurci direban daya daga cikin motocin da ya kai su garin Mpeketoni, inda suka yi ta bude wuta.

Wasu shaidu sun ce 'yan bindigan sun kai hari a wasu Otel-Otel biyu da ofishin 'yan sanda da kuma banki hade da wani gidan sayar da man fetur da ke garin.

Kawo yanzu dai ba a tantance adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su ba, amma kakakin sojin kasar Manjo Eammanuel Chichir ya ce ana amfani da wani jirgin sama mai leken asiri domin gano inda maharan su ke.