''Harin Amurka ya kara rikita Pakistan''

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tuni dai da amfani da jiragen ya jawo kace-nace a Pakistan.

Wani rahoton da aka fitar ranar Litinin ya ce amfanin da jiragen yaki marasa matuka da Amurka ke yi a yankunan kabilu da arewa maso yammacin Pakistan ya taimaka wajen bazuwar ayyukan tarzoma zuwa sauran sassan kasar.

Wadanda suka fitar da rahoton, Oxford Research Group sun ce hare-hare da jiragen wadanda suka karu sosai a shekara ta 2010, sun sa dimbin mayakan Taliban yin kaura zuwa wasu sassan Pakistan domin gujewa hare-haren.

Rahoton dai ya yarda cewa jiragen sun taimaka wajen tarwatsa mayakan Taliban daga yankunan tsirarun kabilu na Pakistan inda doka ba ta aiki abin da ya kai ga wargaza tsare-tsaren masu tsattsauran ra'ayi.

Sai dai Rahoton ya dage kan cewar hakan na da mummunan tasiri mai yawa ga kasar Pakistan.

Karin bayani