Obama zai tura dakaru zuwa Iraki

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Amirka ta tura sojojinta Iraqi a shekarun baya, ko wane tasiri za su yi a wannan lokaci?

Shugaba Obama ya ce Amirka za ta tura dakaru dari biyu da saba'in da biyar kasar Iraqi domin kare muradun Amurka, a daidai lokacin da masu tada kayar baya 'yan Sunni suke ci gaba da kaddamar da hare-hare.

A wata takarda da ya rubutawa shugabannin Majalisar Dokokin Amurka, Mr Obama yace, an ba rundunar makaman yaki ko ta yiwu ya zama dole su shiga fadan.

'' A cikin takardar, Mr Obama yace, za su yi amfani da makaman ne domin kare Amurkawa da dukiyoyinsu da kuma ofishin jakadancin kasar da ke Bagadaza idan bukatar hakan ta kama." In ji wata wakiliyar BBC a birnin Washington.

Dakarun sojin za su ci gaba da kasancewa a Iraqin har sai an shawo kan lamarin matsalar tsaron.

Mayakan kungiyar ISIS da ke son kafa daular Islama a Iraqi da Syria, ta karbe iko da wasu garuruwa da biranen kasar a makon da ya gabata.