Al'adar tsage a fuska a kasar Benin

A wasu sassan Afrika ana tsage a fuska ko kuma a wasu sassan jiki abinda ke nuna al'ada ko kuma kabilar mutum.

Al'adar ta soma gushewa a tsakanin al'umma saboda zamani, sabanin bin irin tsarin iyaye da kakkanni.

A cikin labarin akwai wasu hotunan da za su iya tada hankalin mutane.

A garin Ouidah na kudancin Benin, ana wata al'ada mai suna voodoo wacce ake shafe kwanaki biyu ana yi.

Kabilar Houeda na daga cikin kabilun a Jamhuriyar Benin da ke yi wa yara kananan tsage a fuska, domin hadewa da kakanninsu.

Image caption Genevieve Boko na alfahari na tsage a fuska

Ana baiwa yaran sabbin sunaye, a yi musu aski sannan a kaisu wajen da za su zanta da kakanninsu.

"Hakan na cikin al'adarmu kuma yana da mahimmanci a gare mu," in ji Genevieve Boko wacce aka yi wa diyarta Marina 'yar watanni shida da haihuwa tsage a fuska.

Ana shafa toka a wurin da aka tsaga sannan kuma ba a dadewa wajen yin tsagar.

Image caption Gamba Dahoui ta gaji mijinta wanda wanzami ne

Tun bayan rasuwar mijinta, Gamba Dahoui ta koma yi wa yara tsage, amma kuma tana wanke askar saboda rage yiwuwar yada cuta.

Ana saka gawayi a cikin tsagar don warkewa da wuri.

Dahoui na amfani da aska guda daya wajen yi wa yara daban-daban tsage.

A Nigeria da ke makwabtaka a Benin, batun 'yancin kananan yara ya sa an kafa dokar da ta haramta yi wa yara kananan tsage a wasu jihohin kasar.

Image caption Jariri na kuka ana masa tsage

Amma wannan dokar ba za ta karbu ba a Benin. "Bama take hakkin kananan yara, muna nuna musu inda suka fito ne," in ji Telephore Sekou Nassikou babban edita a gidan rediyon Natitingou ya bayyana.

A cewarsa, tsage a fuska na aika sakon cewar "akwai matsaloli a duniya kuma hakan na cikin rayuwa."