Cutar Ebola ta kashe mutane 7 a Liberia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kwayar cutar Ebola na haddasa mummunan zubar jini da zazzabi mai tsanani

Wani jami'in lafiya a Liberia yace mutane bakwai sun mutu a Liberia, sakamakon cutar Ebola da ta bazu zuwa Monrovia.

Mutanen sun hada da Nas daya da kuma wasu mutane hudu 'yan gida daya.

Annobar cutar Ebola ta hallaka fiye da mutane 250 a yammacin Afirka, kuma ta fara barkewa ne a kasar Guinea a farkon wannan shekarar.

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana annobar a matsayin daya daga cikin cuta mafi muni a tsawon tarihi.

Kungiyoyin agaji na lafiya sun ce dalilin da ya sa cutar ke yaduwa shi ne wasu ba sa yarda da su je asibiti a duba lafiyarsu, inda suke gwammacewa su nemi taimako daga masu maganin gargajiya.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba