Gilashin da ke taimakawa makafi

Image caption Kungiyar ta yi murna da kirkirar gilashin

Masu bincike a Jami'ar Oxford ta Birtaniya sun kirkiri wani tabarau ko gilashin fuska da ke taimakawa mutanen da keda matsalar ido.

Gilashin na taimakawa a iya ganin mutanen da ke kusa ko abubuwan da ba suda nisa kuma suna sa mutum yaga abu rangadau.

Gilashin ya taimakawa wasu mutane sun ga dan rakiyarsu a karon farko.

Cibiyar makafi ta Birtaniya ta ce wannan gilashin "nada matukar mahimmanci".

Lyn Oliver nada matsalar gani, a matsayinta na 'yar shekaru 70 an gwada idonta an gano tana da matsala tun tanada shekaru 20 amma kuma ta soma gani dishi-dishi da wannan gilashin.

Ta ce a yanzu tana iya ganin karen da ke yi mata jagora saboda wannan gilashin.

Kusan mutane miliyan biyu ne a Birtaniya ke da matsalar gani.

Masu binciken na jami'ar Oxford sun ce wannan gilashin da suka kirkira na taimakawa gani.