An soma yunkurin tsige Gwamna Murtala Nyako

Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako Hakkin mallakar hoto google
Image caption An jima ana samun rashin jituwa tsakanin gwamna Nyako da 'yan Majalisar dokokin jihar

Majalisar dokokin jihar Adamawa ta fara yunkurin tsige gwamnan jihar Murtala Nyako da mataimakinsa Bala Ngilari daga kan mukamansu.

A ranar Laraba ne Majalisar ta umarci akawunta da ya mika wa gwamnan da mataimakinsa takardar shirin tsige su.

An dai yi ta samun takun saka tsakanin gwamna Murtala Nyako da 'yan Majalisar dokokin jihar tun bayan da gwamnan ya sauya sheka daga Jam'iyyar PDP zuwa APC.

Yanayin siyasar jihar ya yi zafi ne bayan da Majalisar dokokin ta ba da umarnin tsare wasu kwamishinonin jihar su hudu saboda kin gurfana da suka yi a gaban Majalisar domin su amsa tambayoyi game da yadda ake kashe kudaden gwamnatin jihar.