'Mun kama dan Boko Haram cikin 'yan arewa'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram sun addabi Nigeria

Rundunar tsaron Nigeria ta yi ikirarin kama wani da ta ce babban dan ta'adda ne a cikin mutane 'yan arewacin kasar fiye da dari hudu da ta tsare a jihar Abia na kudancin kasar.

Sai dai rundunar tsaron ba ta yi wani karin bayani ba game da mutumin da ta ce dan Boko Haram ne da take nema ruwa a jallo.

Tun a karshen mako ne hukumomin sojin kasar suka tsare mutane kusan 487 a garin Aba na jihar Abia, tare da gudanar da binciken kan su bisa zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Mutanen wadanda suka fito daga jihohin a Jigawa da Bauchi, an kama su ne a cikin motoci bas-bas 36, a kan hanyarsu ta zuwa birnin Fatakwal na jihar Rivers.

'Yan uwan mutanen sun ce wadanda aka kama din ba 'yan Boko Haram bane, sun je kudancin kasar ne domin ci rani.

Karin bayani