ECOWAS na taro kan Boko Haram

Shugabannin kasashen ECOWAS
Image caption Kasashen yammacin Afrika na fama matsalar tabarbarewar tsaro a yankin.

Ministocin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS na taro a Ghana don tattauna matsalar Boko Haram da ta addabi arewacin Nigeria.

Dubban mutane ne suka rasa rayukansu a hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram ke kai wa a wasu sassa na arewa-maso-gabashin Nigeria.

A baya dai kasashen da ke kungiyar ta ECOWAS sun yi alkawarin hada kai don kawo karshen matsalar tabarbarewar tsaro a yankin.

Kasar Kamaru ta zuba dakaru kimanin 3,000 a bakin iyakarta da Nigeria, a dai dai lokacin da ake ci gaba da nuna fargabar yaduwar ayyukan kungiyar zuwa kasashe makwabta.