Abinci mai guba: Mutane 138 na jinya a Guinea

Conakry babban birnin Guinea
Image caption A cewar mai abinci wasu mutane ne suka sayar mata da bakin mai a matsayin man gyada garwa biyu

A kasar Guinea, mutane kimanin 138 ne aka kwantar a babban asibitin Conakry, babban birnin kasar, sakamakon cin abinci mai guba.

Mutanen dai sun ci wata shinkafa ce da aka dafa da bakin mai na mota.

An ce mutanen sun ci abincin ne a wani karamin gidan abinci dake anguwat Kaloum.

Babu dai wanda ya mutu sakamakon cin abincin mai guba, kuma 'yan sanda na gudanar da bincike a kan lamarin.